Shugaban Kasar Madagaska Ya Bayyana Anniyarsa Ta Shigaban Takarar Shugabancin Kasar
Shugaban kasar Madagaska Hery Rajao-narimam-pianina ya bada sanarwan shiga takarar shugabancin kasar a karo na biyu a karshen wannan shekara
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a babban birnin kasar Antanana Rivo jiya Jumma'a, ya kuma kara da cewa idan an sake zabansa a kan kujerar shugabancin kasar zai ci gaba da aikin kyautata rayuwar mutanen kasar fiye da aikin da ya yi a halin yanzu.
Za'a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Madagaska a ranar 7 ga watan Nuwamba mai zuwa, kuma ya zuwa yanzu yan takara 23 suna yi rigistan shigaa takarar shugabancin kasar. Masu karfi daga cikin yan takarar dai sun hada dai wadanda za su iya yin barazana ga shugaba Hery su ne Andry Rajoelina da kuma aMarc Ravalomanana wadanda suka taba rike kujerar shugabancin kasar. Kofar rijistan yan takara a bude take har zuwa ranar 21 ga watan Auguta da muke ciki.