Majalisar Dattijan Kasar Congo Ta Bukaci Madugun 'Yan Adawa Ya Dawo Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32855-majalisar_dattijan_kasar_congo_ta_bukaci_madugun_'yan_adawa_ya_dawo_gida
Shugaban Majalisar datijan jamhoriyar D/Congo ya bukaci madugun 'yan adawar kasar ya dawo gida domin ya halarci zaben shugaban kasa da za a yi a kasar
(last modified 2018-08-21T14:31:34+00:00 )
Aug 21, 2018 14:31 UTC
  • Majalisar Dattijan Kasar Congo Ta Bukaci Madugun 'Yan Adawa Ya Dawo Gida

Shugaban Majalisar datijan jamhoriyar D/Congo ya bukaci madugun 'yan adawar kasar ya dawo gida domin ya halarci zaben shugaban kasa da za a yi a kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Léon Kengo Wa Dongo shugaban Majalisar dattijan jamhoriyar D/Congo na cewa fitar  Moïse Katumbi madugun 'yan adawa daga kasar saboda wasu na ganin cewa zai iya lashe zabe inda ya tsaya takarar shugabancin kasar ta Congo.

Wa Dongo ya ce duk da cewa Moise Katumbe ya juriya hukuncin dauri na shekaru uku a gidan yari, to amma ya nemi afuyar shugaba Joseph Kabila, sannan a halin da ake ciki kowa nada damar tsayawa takarar shugaban kasar ta Congo, domin mista Katumbe na iya dawo wa kasar domin tsayawa takarar shugabancin kasar.

Kotun kasar Congo ta  yankewa Katumbe hukuncin daurin shekaru uku ne a bayan idanunsa sannan a watan Maris din 2016 ya fice daga kasar inda yanzu haka ke zaune a kasar Zambiya, duk da cewa har yanzu Katumbe bai samu komawar kasarsa ba, to amma ya bayyana aniyarsa na tsayawa takarar shugabancin kasar a watan Dicembar wannan shekara ta 2018.