'Yan Tawayen Uganda Sun Kai Wa sojojin Kasar Demokradiyyar Congo Hari
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32911-'yan_tawayen_uganda_sun_kai_wa_sojojin_kasar_demokradiyyar_congo_hari
Majiyar tsaron kasar ta Demokradiyyar Congo ta ce a jiya asabar ne 'yan tawayen kungiyar ADF ta kai hari akan sojoji tare da kashe daya daga cikinsu
(last modified 2018-08-26T02:42:09+00:00 )
Aug 26, 2018 02:42 UTC
  • 'Yan Tawayen Uganda Sun Kai Wa sojojin Kasar Demokradiyyar Congo Hari

Majiyar tsaron kasar ta Demokradiyyar Congo ta ce a jiya asabar ne 'yan tawayen kungiyar ADF ta kai hari akan sojoji tare da kashe daya daga cikinsu

Wani shedar ganin ido ya ce; A yayin harin da kungiyar ADF ta kai a garin Beni ta fuskanci mayar da martani mai tsanani daga sojojin da su ka kashe 10 daga cikin 'yan tawayen.

Tun a 1994 ne 'yan tawayen kasar Uganda suke kai hare-hare a gabacin kasar Demokradiyyar congo wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane.

Yankunan tsakiya da kuma gabacin kasar ta Demokradiyyar Congo suna a matsayin sansanonin kungiyoyin 'yan tawaye na cikin gida da kuma kasashen makwabta.