Bankin Duniya Zai Bai Wa Kasar Habasha Bashin Makudan Kudade
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32935-bankin_duniya_zai_bai_wa_kasar_habasha_bashin_makudan_kudade
Babban bankin duniya na shirin bayar da wasu makudan kudade da za su kai dala biliyan daya ga gwamnatin kasar Habasha, domin ci gaba da ayyukan kawo gyara da tayar da komadar tattalin arziki.
(last modified 2018-08-27T12:22:58+00:00 )
Aug 27, 2018 12:22 UTC
  • Bankin Duniya Zai Bai Wa Kasar Habasha Bashin Makudan Kudade

Babban bankin duniya na shirin bayar da wasu makudan kudade da za su kai dala biliyan daya ga gwamnatin kasar Habasha, domin ci gaba da ayyukan kawo gyara da tayar da komadar tattalin arziki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a yau Litinin firayi ministan kasar Habasha Abi Ahmad ya sanar da cewa, bankin duniya na shirin zuba dala biliyan daya a cikin babban bankin kasar, domin taimaka ma tsare-tsarenta da kasar take da su a bangaren tattalin mulki tattalin arziki.

Firayi ministan na Habasha ya kara da cewa, kasar za ta ci gaba da abin da ta sanya a gaba a halin yanzu, na yin gyara a bangaren siyasa da kuma tattalin arziki, da hada kan al'ummar kasa, da kuma kyautata dangantaka da sauran kasashen duniya.

Dangane da batun zabukan da za a gudanar a kasar a cikin shekara ra 2020, Abi Ahmad ya bayyana cewa, kofa bude take ga dukkanin 'yan kasa, da kuma jam'iyyun siyasa domin shiga takarar zabe.