Faduwar Jirgin Saman Sojin Kasar Habasha Ta Lashe Rayukan Mutane 21
Aug 30, 2018 14:43 UTC
Rundunar sojin Habasha ta sanar da cewar wani jirgin rundunar sojin kasar kirar helikobta ya fado kasa lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 21.
Rundunar sojin kasar Habasha a yau Alhamis ta sanar da cewa: Wani jirgin saman rundunar sojin kasar kirar helikobta ya rikito kasa a yankin Lumi da ke gabashin kasar, inda aka samu hasarar rayukan mutane 21 kuma 17 daga cikinsu sojoji ne gami da wasu mata biyu da kananan yara biyu.
Rundunar sojin ta Habasha ta kara da cewa: Jirgin ya taso ne daga garin Dire Dawa da ke gabashin kasar zuwa garin Bishoftu da ke nisan kilomita 48 da birnin Adis-Ababa fadar mulkin kasar.