Habasha: Zaizayar Kasa Ta Ci Rayukan Mutane 12
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33058-habasha_zaizayar_kasa_ta_ci_rayukan_mutane_12
Kafafen watsa labarun kasar Habasha sun ba da labarin cewa kimanin mutane 12 ne suka kwanta dama sanadiyyar zaizayar kasa a yankin arewa maso yammacin kasar
(last modified 2018-09-05T07:20:56+00:00 )
Sep 05, 2018 07:20 UTC
  • Habasha: Zaizayar Kasa Ta Ci Rayukan Mutane 12

Kafafen watsa labarun kasar Habasha sun ba da labarin cewa kimanin mutane 12 ne suka kwanta dama sanadiyyar zaizayar kasa a yankin arewa maso yammacin kasar

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato kafafen watsa labarun kasar ta Habasha suna cewa; Wasu mutane 4 sun jikkata sanadiyyar zaizayar kasar a yankin Isara.

Kawo ya zuwa yanzu an fito da gawawwakin mutane 10, yayin da ake ci gaba da kokarin fito da sauran.

A duk lokacin damina kasar ta Habasha tana fama da matsalar zaizayar kasa wanda kan haddasa asarar rayuka

A cikin watan Mayu na wannan shekarar ma mutane 32 ne su ka rasa rayukansu a kudancin kasar.