An Ceto Bakin Haure Sama Da 400 A Arewacin Kasar Nijer
Hukumar dake kula da 'yan gudun hijra ta MDD ta ce cikin kwanaki biyu ta ceto bakin haure sama da 400 a cikin yankin Sahara na kasar Nijer dake kan iyaka da kasar Aljeriya
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto hukumar kula da 'yan gudun hijra ta MDD cikin shafin sadarwarta na Fecebook ta wallafa cewa 'yan gudun hijra 439 ne da suka tako daga kasar Aljeriya da kafafuwansu zuwa yankin saharar na lardin Asamaka na jamhoriyar Nijer mai iyaka da Aljeriya .
Hukumar ta ce baya isowar wadannan mutane sun sanar da ceto cewa akwai wasu da dama da suka mallake a cikin saharar ,inda a ranar 3 ga wannan wata na Satumba da muke ciki, ta tura tawaga bincike zuwa yankin saharar na arewacin jamhoriyar Nijer dake kan iyaka da kasar Aljeriyan, inda suka ceto bakin haure 347 na kasashen 13 na yammacin Afirka.
Har ila yau, majiyar ta ce ko baya ga wadannan mutane akwai wasu bakin haure 92 a ranar 4 ga wannan waasn satumba, inda jami'an kai agajin gaggawa na hukumar suka ceto su.
A tsakiyar watan Augustan da ya gabata ma, an ceto bakin haure 128 daga cikinsu akwai mata takwas da kananen yara 14 a kusa da kan iyakar Nijer da Aljerian.