An Gudanar Da Taro Kan Matsalar Karamcin Abinci A Afirka
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33083-an_gudanar_da_taro_kan_matsalar_karamcin_abinci_a_afirka
A cikin wannan mako ne kwararru a fannin harkokin noma na Afirka suka gudanar da taro a birnin Kigali , inda suka yi gargadin cewa matsalar sauyin yanayi da kuma yaduwar tsutsotsi na barazanar haddasa matsalar karancin abinci a Nahiyar Afirka.
(last modified 2018-09-07T07:41:38+00:00 )
Sep 07, 2018 07:41 UTC
  • An Gudanar Da Taro Kan Matsalar Karamcin Abinci A Afirka

A cikin wannan mako ne kwararru a fannin harkokin noma na Afirka suka gudanar da taro a birnin Kigali , inda suka yi gargadin cewa matsalar sauyin yanayi da kuma yaduwar tsutsotsi na barazanar haddasa matsalar karancin abinci a Nahiyar Afirka.

Kwararrun sun ce nau'in tsutsar nan zunkudau da ta samo asali daga kasashen Latin Amirka da kuma aka gano yaduwarta a kasashen Afirka a shekara ta 2016, yanzu haka na yaduwa kamar wutar daji inda tuni aka gano ta a kasashe 44 daga cikin kasashen nahiyar Afirka sabanin kasashe 28 a shekarar da ta gabata. 

Kwararrun sun kiyasta cewa mutane sama da miliyan 300 ne ka iya fuskantar barazanar karancin abinci a shekarar ta bana a sakamakon wannan tsutsa da sauran kwarin wanda babu wani nau'i na shuka da ba sa far ma wa.