Tarayyar Afirka Ta Nuna Goyon Bayanta Akan Sulhu Tsakanin Habasha Da Eritrea
Shugaban hukumar tarayyar Afirka Musa Faki Muhammad ne ya bayyana goyon bayan ga kokarin warware sabani a tsakanin kasashen Habasha da Eritrea
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato Musa Faki Muyhammad Yana cewa; Sauye sauyen da ake samu a gabacin Afirka na sulhu tsakanin kasashe abin a yaba da shi ba.
Kasashen Habasha da Eritrea sun mayar da huldar diplomasiyya a tsakaninu a ranar 16 ga watan Yuni wanda shi ne na farko a cikin shekaru ashirin na alakar kasashen biyu mai cike da sabani.
Shugaban kasar Eritrea Isaias Afewerki ne ya halarci bikin bude ofishin jakadancin kasar tashi a Addis Ababa.
Ita ma kasar Habashan ta tura jakadanta na farko Rezvan Husain zuwa kasar Eritrea a ranar 19 g awatan na Yuni.