Wadanda Suka Rasu Sanadiyar Cutar Ebola Ya Karu A Kasar D/Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33168-wadanda_suka_rasu_sanadiyar_cutar_ebola_ya_karu_a_kasar_d_congo
Ma'aikatar kiyon lafiya ta jahmhoriyar Demokaradiyar Congo ta sanar da cewa adadin mutanan da suka rasa rayukansu sanadiyar cutar Ebola ya haura zuwa 92.
(last modified 2018-09-13T14:46:18+00:00 )
Sep 13, 2018 14:46 UTC
  • Wadanda Suka Rasu Sanadiyar Cutar Ebola Ya Karu A Kasar D/Congo

Ma'aikatar kiyon lafiya ta jahmhoriyar Demokaradiyar Congo ta sanar da cewa adadin mutanan da suka rasa rayukansu sanadiyar cutar Ebola ya haura zuwa 92.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan alhamis, ma'aikatar kiyon lafiya ta kasar Demokaradiyar Congo ta ce daga farkon watan Augusta zuwa yanzu, mutum 133 ne suka kamu da cutar ebola a kasar, daga cikinsu kuma mutum 92 ne suka rasa rayukansu.

Tun a watan Mayun da ya gabata ne cutar Ebolar ta sake billa a garin Bikoro na jahar Équateur dake arewa maso yammacin kasar ta Congo sannan  ta wanzu zuwa garin Mbandaka na tsakiyar jahar kafin daga bisa ta sake wanzuwa zuwa yankunan gabashin kasar ta Congo.

Daga shekarar 2014 zuwa yanzu cutar ta Ebola ta billa har so uku a kasar Demokaradiyar ta Congo.

Daga shekarar 2013 zuwa 2016, cutar ta ebola ta salwanta rayukan mutane kimanin dubu 11 a wasu kasashe na yammacin Afirka.