Mutane Kimani 55 Ne Suka Rasa Rayukansu Saboda Cutar Kolera A Niger
Majalisar dinkin duniya ta bada labarin cewa mutane akalla 55 ne suka rasa rayukansu saboda bukkar cutar Kolera a kudancin kasar.
Majiyar muryar jumhuriyar Musulunci ta Iran ya nakalto majalisar tana bada wannan labarin ne a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa cutar ta fi barna a yankin Maradi na kudancin kasar sannan tana kara yaduwa zuwa wasu wuraren.
Rahoton ya kara da cewa tun watan Yunin da ya gabata ne cutar ta mulla sannan ya zuwa yanzu ta mkama mutane 2,782.
A ranar 15 ga watan Augustan da ta gabata, ma'aikatar Lafiyar kasar ta Niger ta bada sanarwan cewa mutane 22 suka rasa rayukansu sanadiyarr cutar.
Cutar kolera dai cuta ce wacce take yaduwa kuma takan sanya zawo, wanda zai haddasa karancin ruwa a jikin mutum, idan kuma ba'a gaggauta magance shi da sauri ba to kuwa zai iya kaiga mutuwa.
Cin gurbataccen abinci ko ruwansa ne suke haddasa cutar Kolera, kuma tana bulla ne a wuraren da babu tsabata.