'Yan Bindiga Sun Kai Hari A Gabashin Burkina Faso
Wasu 'yan bindiga da ake zaton masu da'awar jihadi ne sun kai hare-hare a gabashin kasar Burkina Faso inda suka kashe mutane akalla 8, tare da jikkata wasu.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, maharan sun kai hare-haren ne a garuruwan Diabiga da kuma Kompienbiga da suke a gabashin kasar ta Burkina Faso, inda suka kashe fararen hula akalla 8 a daren juma'a zuwa kashe garin jiya Asabar, kuma sun tsere ba tare da kame ko daya daga cikinsu ba.
Kasar Burkina Faso ta fara fuskantar hare-haren ta'addanci ne daga kungiyoyin 'yan salafiyya masu tsatsauran ra'ayi da ke da'awar jihadi a cikin shekarun baya-bayan nan.
Mahukunta a kasar dai na bayyana cewa mafi yawan 'yan ta'addan da suke aikata wannan ta'adi suna shigowa cikin kasar ne daga kasar Mali da ke makwabtaka da kasar.