Rikici Ya Hallaka Mutum 9 A Birnin Tripoli Na Kasar Libiya
Akalla mutum 9 suka hallaka yayin da wasu 13 na daban suka samu rauni sakamakon musayar wuta tsakanin kungiyoyin matasa dake dauke da makamai a Tripoli babban birnin kasar Libiya
Kakakin cibiyar kula da ayyukan jin kai a fannin kiwon lafiya a birnin Tripoli fadar mulkin kasar Libiya Isamah Ali ya bayyana cewa: Dauki ba dadi tsakanin kungiyoyin dake dauke da makamai a birnin Tripoli fadar mulkin Libiya a daren jiya alhamis ya salwanta rayukan mutum 9, 4 daga cikinsu fararen hula ne.
Tun a ranar Lahadi 9 ga watan Augustan da ya gabata, kungiyoyin 'yan bindiga suke dauki da badi a birnin Tripoli, a ranar 9 ga wannan wata na satumba da muke ciki an cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta bisa shiga tsakanin tawagar Majalisar Dinkin Duniya, to saidai yarjejjeniyar ba taje ko ina ba.
Daga farkon fara rikicin zuwa yanzu, rayukan mutum 78 ne suka salwanta yayin da wasu 313 suka samu rauni.
Tun a shekarar 2011 ne kasar Libiya ta fada cikin rikici bayan juyin milkin da 'yan tawaye bisa goyon bayan Amurka da kungiyar tsaron Nato suka yi wa marigayi kanal Mu'amar Kaddafi, lamarin da ya sanya 'yan ta'adda daga sassa daban daban na Duniya suka kafa sansaninsu a kasar.