Tanzania: Mutane 44 Sun Mutu A Tafkin Victoria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33272-tanzania_mutane_44_sun_mutu_a_tafkin_victoria
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ce a jiya alhamis ne jirgin ruwan mai suna Nyerere ya nutse da mutanen a cikin tsibirin Yokara da ke kudancin tafkin Victoria
(last modified 2019-01-16T04:00:45+00:00 )
Sep 21, 2018 07:45 UTC
  • Tanzania: Mutane 44 Sun Mutu A Tafkin Victoria

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya ce a jiya alhamis ne jirgin ruwan mai suna Nyerere ya nutse da mutanen a cikin tsibirin Yokara da ke kudancin tafkin Victoria

An tseratar da mutane 37 daga cikin mutanen da suke cikin jirgin ruwan yayin da 44 suka rasa rayukansu.

Gwamnatin Tanzania ta sanar da cewa abu ne mai yiyuwa a sami karuwar adadin wadanda ruwan ya ci.

Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan dalilin nutsewar jirgin ruwan na Nyerere, sai dai mafi yawancin hatsura irin wadannan da suke faruwa a cikin tafkin na victoria suna da alaka ne da tsufan jiragen ruwan da suke jigilar mutane ko kuma daukar mutane fiye da kima.

A baya a shekarar 1996 mutane 700 ne ruwa ya ci a tafkin na vivtoria, yayin da wasu 60 su ka rasa rayukansu a 2012, sai kuma wasu 20 a 2016.