Mozambique: Mutane 12 Sun Mutu Sanadiyyar Harin Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33281-mozambique_mutane_12_sun_mutu_sanadiyyar_harin_ta'addanci
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambato cewa harin da wata kungiyar 'yan ta'adda ta kai a arewacin kasar Mozambique ya ci rayukan mutane 12 da kuma jikkata wasu 14.
(last modified 2018-09-22T03:00:37+00:00 )
Sep 22, 2018 03:00 UTC
  • Mozambique: Mutane 12 Sun Mutu Sanadiyyar Harin Ta'addanci

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ambato cewa harin da wata kungiyar 'yan ta'adda ta kai a arewacin kasar Mozambique ya ci rayukan mutane 12 da kuma jikkata wasu 14.

Bugu da kari kungiyar 'yan ta'addar ta tashi gobara a cikin gidaje 55 a kauyen Pequeue a kusa da tsibirin Quirimbas a arewacin kasar ta Mozambique.

Daga lokacin bayyanar wannan kungiyar a 2017, wannan shi ne hari mafi muni da ta kai a cikin kasar.

Kungiyar ta kunshi masu tsauran ra'ayi, da mutanen kasar su ke ba su sunan Shaba. Ya zuwa yanzu kungiyar ta kashe fararen hula 50 da kuma kona kauyuka masu yawa.