Gwamnatin Habasha Ta Rufe Kurkukun Ogaden
Sep 23, 2018 08:17 UTC
Gwamnatin yankin somali na kasar habasha ta bada sanarwan rufe mummunan korkukun kasar wanda aka fi sani da kurkukun Ogade
Jaridar Afrikanews ya nakalto majiyar gwamnatin kasar Habasha na cewa gwamnatin lardin Somali a kasar ta Habasha ta rufe kurkukun Ogaden wanda ya shahara da azabtar da mutane a cikinsa.
Kungiyar kare hakkin bil'adama Human right wash ta dade tana sanya ido a kan wannan kurkukun wanda aka kafa shi tun lokacin shugabancin Abdi Mahammad wanda yake azabtar da yan tawayen Odade wadanda aka haramta kungiyar su. A halin yanzu dai kotun kasa da kasa ta ICC tana bin tsohon shugaban kasan don taken hakkin bil'adama sanadiyar wannan kurkuku.