Al'ummar Zambiya Ta Gudanar Da Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Gwamnatin Kasar
Sep 29, 2018 08:27 UTC
Daruruwan jama'a a Zambiya sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da yadda barnata dukiyar kasa da yin sama da fadi da ita suka yi kamari a kasar.
Rahotonni daga Zambiya sun bayyana cewa: Daruruwan jama'a a birnin Lusaka fadar mulkin kasar ta Zambiya a jiya Juma'a sun gudanar da zanga-zangar lumana tare da yin gangami a kofar Majalisar Dokokin Kasar suna rera taken yin Allah wadai da yadda barnata duniya kasa da yin zama da fadi da ita suka wurga al'ummar kasar cikin mummunan halin talauci.
Har ila yau masu zanga-zangar sun jaddada bukatar ganin mahukuntan Zambiya sun hanzarta daukan matakin gaggawa domin shawo kan matsalar sace kudin gwamnati da wasu 'yan tsiraru ke yi.