Mayakan Boko Haran Sun Kashe Mutane 6 A Yankin Tabkin Chadi
Majiyar labarai daga kasar Chadi sun bayyana cewa mayakan Boko Haram Sun Kashe Mutane 6 A yankin Tabkin Chadi.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto majiyar jami'an tsaron kasar Chadi tana fadar haka a yau Asabar, ta kuma kara da cewa a fafatawa tsakanin jami'an tsaron kasar da Mayakan Boko Haram da suka kai hari kan garuruwan Musarom da Ngueleya wadanda suke kudancin garin Baga Sola an kashe sojojin Chadi biyu, mayakan boko Haram 3 da kuma jami'in Custom ko Duwan guda.
Majiyar ta kara da cewa sojojin kasar Chadi sun sami nasarar kashe yan ta'adda 17 a wani fafatawa na daban. Bayan harin dai mayakan na Boko Haram sun janye daga wadanan yankuna.
Yankin tabkin chadi yanki ne wanda yake tsakanin kasashen Najeriya, Niger, Kamaru da kuma Chadi. Mayakan boko haram, daga lokaci zuwa lokaci su kan yi amfani da yankin don kai hare-haren a cikin kasashen 4.