'Yan Adawa Sun Gudanar Da Gagarimin Gangami A Kasar D/Congo
Duban mutane sun amsa kiran 'yan adawa a kinshasa babban binrnin kasar Demokaradiyar Congo.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya asabar dubun dubatan mutane ne suka amsa kirar shugabanin 'yan adawa a wani taron gangami a aka gudanar a birnin Kinshasa, wanda ya samu halarta 'yan takarar shugaban kasa 4.
A yayin da yake gabatar da jawabi, Jean-Pierre Bemba da hukumar zaben kasar ba ta tattance takararsa ba, ya gargadi gwamnatin Joseph Kabila a kan duk wani yunkuri na magudi a zaben shugaban kasar da za a yi karshen wannan shekara da muke ciki.
Har ila yau 'yan adawar sun nuna rashin amincewarsu da shirin gwamnati na samar da wasu motoci da za a kada kuri'a a cikinsu, inda suka bayyana hakan da cewa wani yunkuri ne na gudanar da magudi a zaben.
Kundin tsarin milki na kasar ta Congo ya haramtawa Shugaba Joseph Kabila sake tsayawa takara a karo na uku, inda ya bayyana Emmanuel Ramazani Shadary tsohon ministan cikin gida na kasar a matsayin dan takararsa.
A ranar 23 ga watan Dicembar 2018 ne za a gudanar da zaben Shugaban kasa a jamhoriyar Demokaradiyar Congo.