An Dakatar Da Ayyukan Kungiyoyin Kasashen Waje A Burundi
Gwamnatin kasar Burundi ta dakatar da ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen waje da ke ayyuka a kasarta har na tsawon watanni uku daga daya ga watan Oktoba mai kamawa.
Ofishin fadar shugaban kasar ta Burundi ya sanar a jiya assabar cewa an dauki wannan mataki ne har lokacin da dokar da ta kayyade ayyukan kungiyoyin za ta soma aiki.
Bayan dai wani bincike ne da kwamitin tsaro na kasar ta Burundi ya gudanar kan ayyukan kungiyoyin, ya gano cewa akasarin kungiyoyin ba su bin dokokin kasar ta Burundi kaman yadda babban sakataran gudanarwa na kwamitin tsaron kasar Janar Sisas Ntigurirwa ya sanar yayin wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin na kasar ,
Sanarwar ta ce sake komawar kungiyoyin kan ayyukansu zai ta'allaka ne ga yadda suka aminta da sabuwar dokar. Sai dai tuni wasu jami'an diflomasiyya ke nuna shakkunsu kan lamarin , ganin cewa wannan sabon matakin da gwamnatin ta Burundi ta dauka ka iya sanya wasu kungiyoyin su rufe ma'aikatunsu a kasar.