An Kashe Fararen Hula Biyu A Gabacin Demokradiyyar Congo
Majiyar sojan kasar Demokradiyyar Congo ce ta sanar da mutuwar fararen hular biyu a wani fada da ya barke a gabacin kasar.
Kamfanin dillancin labarun Anatoli da ya dauko labarin ya kara da cewa; An yi fadan ne a yankin Makoko a tsakanin sojojin kasar da kuma mayakan kungiyar 'yan tawayen kasar Uganda da ake kira ADF a takaice.
Tun a shekarar 1995 kungiyar 'yan tawayen kasar ta Uganda ta ke da sansani a gabacin kasar Demokradiyyar Congo, inda take tsallakawa kan iyaka domin fada da gwamnatin Yawure Masuveni da zummar kifar da ita.
Gwamnatin kasar Demokradiyyar Congo tana zargin kungiyar 'yan tawayen da yi wa dubban fararen hula kisan gilla a gabacin kasar tun daga watan Oktoba na 2014.
A shekarar bara a cikin watan Oktoba kungiyar ta kai hari akan sansanin sojojin Majalisar Dinkin Duniya a yankin tare da kashe 15 daga cikinsu.