Kungiyar Polisariyo Ta Yi Maraba Da Gayyatar Zaman Tattaunawa A Geneva
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33426-kungiyar_polisariyo_ta_yi_maraba_da_gayyatar_zaman_tattaunawa_a_geneva
Tashar talabijin din "Rusiyal-Yaum" ta ambato jagoran kungiyar ta Polisariyo Muhammad Khudad yana cewa: Kungiyar ta yi maraba da gayyatar da MDD ta yi musu na zama domin tattaunawa
(last modified 2018-10-01T09:13:49+00:00 )
Oct 01, 2018 09:13 UTC
  • Kungiyar Polisariyo Ta Yi Maraba Da Gayyatar Zaman Tattaunawa A Geneva

Tashar talabijin din "Rusiyal-Yaum" ta ambato jagoran kungiyar ta Polisariyo Muhammad Khudad yana cewa: Kungiyar ta yi maraba da gayyatar da MDD ta yi musu na zama domin tattaunawa

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya akan rikicin sahara  Host Kohler ne ya gayyaci kungiyar da ta halarci tattaunawar Geneva a ranakun 4 da 5 ga watan Disamba wanda kuma zai kunshi kasashen Maroko da Aljeriya da Murtaniya.

Majalisar Dinkin Duniyar ta bukaci dukkanin bangarorin da aka gayyata da su bayyana matsayarsu daga nan zuwa 20 ga wannan wata na Oktoba.

Yammacin sahara da ke gabar tekun Atlantika, yana a matsaytin yaki daya da ya saura ake takardama akan makomarsa a nahiyar Afirka, tun bayan kawo karshen mulkin mallaka.

Yankin ya kasance a karkashin mulkin mallakar kasar Spain, sannan kuma a 1975 Moroko ta shimfida ikonta akansa. Mazuna yankin na son a basu damar ayyana makomarsu ta cin gashin kai.