Rikicin Siyasa Ya Kunno Kai Tsakanin Kasashen Moroko Da Netherland
Rikicin siyasa da ya kunno kai tsakanin kasashen Moroko da Netherland ya sanya ministan shari'ar kasar Moroko ya dage tafiyarsa zuwa birnin Amsterdam fadar mulkin kasar ta Netherland.
Wani jami'i a ma'aikatar shari'ar kasar Moroko da ya nemi a sakaye sunansa a yau Talata ya bayyana cewa: Muhammad Aujjar ministan shari'a a Moroko ya fasa gudanar da ziyarar aikin da ya shirya yi zuwa birnin Amsterdam na kasar Netherland domin nuna rashin amincewarsa kan matakin da ministan harkokin wajen kasar Netherland ya dauka na sukar kasar Moroko.
Jami'in ma'aikatar shari'ar kasar ta Moroko ya fayyace cewa: Muhammad Aujjar ministan shari'ar Moroko ya dauki matakin janye gudanar da ziyarar aikinsa zuwa birnin Amsterdam ne saboda bayyana rashin jin dadinsa kan rahoton da ministan harkokin wajen kasar Netherland Steve Blank ya mikawa Majalisar Dokokin Kasarsa da a ciki ya yi kakkausar suka kan yadda mahukuntan Moroko suke musgunawa al'ummar Rif da ke shiyar arewa maso yammacin kasar ta Moroko saboda zanga-zangar da suke yi kan nuna rashin amincewarsu da kisan gillar da aka yi wa wani mutum mai sayar da kifi a garin Al-Hoseima.