An Hallaka 'Yan tawaye 4 A Gabashin jamhoriyar Dimokaradiyar Congo
Dakarun Tsaron kasar Congo sun sanar da hallaka 'yan ta'adda 4 a yayin wani farmaki da suka kai sansani soja na gabashin kasar.
Majiyar tsaron kasar Dimokaradiyar Congo ta sanar a wannan laraba cewa a jiya talata Sojojin kasar sun samu nasarar dakile wani harin 'yan tawayen Mai-Mai da suka kai kan sansanin Sojoji na gabashin kasar, inda suka hallaka 4 daga cikin su.
Rahoton ya ce a yayin arcewar 'yan tawayen, sun yi awan gaba da gawawwakin wadanda aka hallakar, to saidai a yayin da sojojin suka bi bayansu, sun tsinci gawawwakin a yankin Beni na jahar Kivo ta arewa dake gabashin kasar.
A ranar 22 ga watan Satumbar da ya gabata ma 'yan tawayen kasar Uganda sun kai hari gabashin kasar ta Congo , inda suka kashe fararen hula 14 tare da sojoji guda 4.
Daga makoni biyu da suka gabata zuwa yanzu, kungiyoyin 'yan tawaye sun tsananta kai hare-hare a kan sansanin Sojojin kasar Congo a yankunan gabashi da arewa maso gabashin kasar.