Rikicin Kabilanci Ya Salwanta Rayukan Mutum 44 A Habasha
Akalla mutane 44 ne suka rasa rayukansu sanadiyar rikicin kabilanci a yammacin kasar Habasha.
Majiyoyin kasar Ethiopia sun sanar a jiya Talata cewa a farkon makon nan wani sabon rikicin kabilanci ya barke tsakanin mazauna yankunan Oromia da Benishangul-Gumuz a yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum 44.
Rahoton ya ce rikicin ya fara ne a yayin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka hallaka shugabanin yankin Benishangul-Gumuz a yankin Oromia a yayin da suka isa yankin domin tattauna yanayin tsaro a yankunan biyu dake makwabtaka da juna.
A yayin wannan rikici, kungiyoyin matasan bangarorin biyu sun amfani da duwatsu, da sanduna gami da yukake wajen farwa junansu.
A cewar hukumomin yankin, wannan rikici dai ya tilastawa duban al'ummar yankin barin wuraren taruwa da wuraren ayyukansu, da gidajensu.
Rikici tsakanin mazauna yankunan biyu ya samo asali ne tun a shekarar 2015, bayan da aka kwacewa wasu manoma filayen nomansu a yankin.