An Tsawaita Doka Ta Baci A Kasar Tunisia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33502-an_tsawaita_doka_ta_baci_a_kasar_tunisia
Ofishin shugaban kasa a kasar Tunisia ya bada sanarwan tsawaita doka ta baci a kasar na tsawon watan guda.
(last modified 2018-10-06T03:14:19+00:00 )
Oct 06, 2018 03:14 UTC
  • An Tsawaita Doka Ta Baci A Kasar Tunisia

Ofishin shugaban kasa a kasar Tunisia ya bada sanarwan tsawaita doka ta baci a kasar na tsawon watan guda.

Kamfanin dillancin labaran Mehr na kasar Iran ya nakalto sanarwan tana cewa doka ta bacin zata fara aiki ne tun ranar litinin 8 watan Octoban da muke ciki na tsawon wata guda. Labarin ya kara da cewa shugaban kasar ta Tunisia Mohammad Beji Essebsi ya dau wannan matakin ne bayan tattaunawa da ma'aikatar cikin gida da na tsaron kasar. A ranar 12 ga watan Maris na shekara ta 2018 ne shugaba essibcsi tsawaita doka ta baci a kasar na tsawon watanni 7. 

Tun ranar 24 ga watan Nuwamban shekara ta 2015 ne, bayan wani harin da yan ta'adda suka kaiw wata motar Bus dauke da sojojin kasar a birnin Tunis babban birnin Kasar wanda ya kai ga mutuwar mutane 38, 12 daga cikinsu yan sanda ne. Kungiyar yan ta'adda ta Daesh ta dauki nauyin harin yan ta'adda.