Shugaba Buhari Ya Bukaci Ministan Sadarwa Ya Yi Murabus
Wasu majiyoyin fadar shugaban kasar Najeriya sun bayyana cewa shugaban ya bukaci ministan sadarwa Alhaji Adebayo Shittu ya yi murabus daga mukaminsa sanadiyar kasawarsa na yin hidimar kasa na tilas bayan kammala jami'a.
Jaridar Punch ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya fadawa ministan kan cewa kada ya jira sai ya yi masa kamar yadda ya yi wa ministan kudi a kwanakin baya.
Kafin haka dai ministan ya yi hira da kafafen yada labarai inda ya bayyana cewa bayan ya kammala jami'a a zabe shi a majalisar dokokin kasar don haka a dauki hakan a matsayin bautar kasa don haka ne bai shiga shirin ba.
Amma jam'iyyarsa ta APC ta hana shi shiga takarar gwamna a jiharsa saboda rashin aikin na bautar kasa ta tials.
A lokacinda jaridar Punch ta tuntubi ministan ya musanra cewa shugaban kasa ya ce masa ya yi murabus. Kuma ya ce zai yi jawabi ga yan jaridu a mako mai zuwa.