An Yi Gargadi A Kan Wanzuwar Cutar Ebola A Kasar D/Congo.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33619-an_yi_gargadi_a_kan_wanzuwar_cutar_ebola_a_kasar_d_congo.
Ma'aikatar kiyon lafiya ta kasar D/Congo ta yi gargadi kan wanzuwar cutar ebola zuwa yankunan gabashin kasar
(last modified 2018-10-14T08:38:20+00:00 )
Oct 14, 2018 08:38 UTC
  • An Yi Gargadi A Kan Wanzuwar Cutar Ebola A Kasar D/Congo.

Ma'aikatar kiyon lafiya ta kasar D/Congo ta yi gargadi kan wanzuwar cutar ebola zuwa yankunan gabashin kasar

A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya assabar ma'aikatar kiyon lafiya ta kasar D/Congo ta ce dagulewar al'amuran tsaro da rashin aiki tare na Al'umma ya janyo wanzuwar cutar ebola cikin sauri a cibiyar jihar Kivo ta arewa dake gabashin kasar.

Ma'aikatar kiyon lafiya ta ce yanayin da yankin ke ciki, abin damuwa, sannan rashin bayar da hadin kai ga ma'aikatan kiyon lafiya da aka tura  ya kara taimakawa wajen wanzuwar cutar ta ebola cikin sauri.

Wannan dai shi ne karo na tara da cutar ebolar ta billa a kasar D/Congo tun bayan da aka gwanota karan farko a shekarar 1970.