An Kama Mutum 20 Kan Laifin Garkuwa Da Mutane A Tanzania
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33623-an_kama_mutum_20_kan_laifin_garkuwa_da_mutane_a_tanzania
A Tanzania hukumomin kasar sun sanar da capke mutane 20 da ake zaton suna da hannu wajen sace hamshakin mai kudin kasar Mohammed Dewji.
(last modified 2018-10-14T08:40:09+00:00 )
Oct 14, 2018 08:40 UTC
  • An Kama Mutum 20 Kan Laifin Garkuwa Da Mutane A Tanzania

A Tanzania hukumomin kasar sun sanar da capke mutane 20 da ake zaton suna da hannu wajen sace hamshakin mai kudin kasar Mohammed Dewji.

Cikin wata sanarwar da Ministan cikin gidan kasar Kangi Lugola ya fitar a jiya asabar yayin  wata ganawa da manema labarai ya jaddada cewa yan sanda na ci gaba da bincike don gano mutanen da suka kitsa wannan awon gaba da wannan hamshakin Dan kasuwa.

Ministan ya ce bai kamata a ce har yanzu babu labarin Mohammed Dewji ba, shidai wannan Dan tahaliki  mai shekaru 43 a Duniya ya riki  mukamin dan majalisa  daga shekara ta 2005 zuwa 2015,bayan tarin  dukiyar da yake da ita da aka kiyasta cewa ta kai  Triliyan 1 da dugo 29 na euros.

A safiyar Alhamis din da ta gabata aka sace Mohammed Dewji a yayin dake yake kan hanyarsa na shiga filin wasa dake cikin wani katafaran Hotel na birnin Dar-assalam.