An Cimma Yarjejeniyar Tattalin Arziki Tsakanin Najeriya Da Aljeriya
Ministocin Kasashen waje na Najeriya da Aljeriya sun cimma yarjejeniyar aiki tare a bangaren tattalin arziki.
Ministan kasar Aljeriya Abdelkader Messahel da takwaransa na kasar Najeriya Geoffrey Onyeama sun sanya hanu kan yarjejeniyar aiki tare a bangaren tattalin arziki, musaman ma kan batun Makamashi da sufuri da harakokin sadarwa a jiya Litinin.
Bayan sanya hanu kan wannan yarjejjeniya, Ministan harakokin wajen Aljeriya ya bayyana cewa kasashen biyu za su gudanar da wadannan muhiman ayyukan tare, sannan ya ce za su gida babbar hanya wacce za tashi daga birnin Alje na kasar Aljeriya zuwa birnin Lagos na Najeriya, baya ga haka, za a shinfita bututun iskar gas na Najeriya wanda zai bi ta cikin kasashen Nijer da Aljeriya har zuwa kasashen Turai.
Shinfida wannan bubutun iskar Gaz tsakanin buranan Legas da Aljeriya zai ci kilomita dubu 4 da dari 4 kuma tuni aka sanya hanun jari na dala biliyan 12 domin fara wannan aiki.