'Yan Tawayen Uganda Sun Hallaka Mutane 11 A Gabashin D/Congo.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33727-'yan_tawayen_uganda_sun_hallaka_mutane_11_a_gabashin_d_congo.
Kimanin mutun 11 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da 'yan tawayen kasar Uganda suka kai gabashin D/Congo.
(last modified 2018-10-21T15:30:17+00:00 )
Oct 21, 2018 15:30 UTC
  • 'Yan Tawayen Uganda Sun Hallaka Mutane 11 A Gabashin D/Congo.

Kimanin mutun 11 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da 'yan tawayen kasar Uganda suka kai gabashin D/Congo.

Hukumomin tsaron jamhoriyar Demokaradiyar Congo sun sanar a wannan Lahadi cewa 'yan tawayen kasar Uganda sun hari Garin Beni na jahar Kivo ta arewa dake gabashin kasar, inda akalla suka hallaka mutum 11 tare da sace wasu 15 na daban daga cikinsu akwai kananen yara 10.

Kafin hakan dai Dakarun Wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun sanar da musayar wuta tsakanin da 'yan tawayen a garin Beni, to saidai ba a samu asarar rayuka ba.

Daga watan Oktoban 2014 zuwa yanzu ana zargi 'yan tawayen kasar Ugandan da kashe dariruwan fararen hula a gabashin jamhoriyar demokaradiyar Congo.

Har ila yau an gano cewa 'yan tawayen na Uganda suke da alhakin kisan dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD 15 a watan Dicembar 2017 a kan iyakar kasar da Uganda.