Habasha Ta Kulla Yerjejeniyar Sulhu Da Kungiyar Yan Tawaye Ta ONLF
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33751-habasha_ta_kulla_yerjejeniyar_sulhu_da_kungiyar_yan_tawaye_ta_onlf
Gwamnatin kasar Habasha ta kulla yerjejeniyar sulhu tare da yan tawayen kasar na kungiyar "Ogaden National Liberation Front" (ONLF).
(last modified 2018-10-23T03:04:28+00:00 )
Oct 23, 2018 03:04 UTC
  • Habasha Ta Kulla Yerjejeniyar Sulhu Da Kungiyar Yan Tawaye Ta ONLF

Gwamnatin kasar Habasha ta kulla yerjejeniyar sulhu tare da yan tawayen kasar na kungiyar "Ogaden National Liberation Front" (ONLF).

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP ya ce gwamnatin Fraiminista Abiy Ahmad ne ya bayyana haka a jiya Litinin ta kuma kara da cewa tawagar gwamnatin kasar Habasha wadda ta hada da ministan harkokin wajen kasar Workneh Gebeyehu sun hadu da shuwagabannin yan tawayen a birnin Asmara na kasar Eritrea a ranar lahadin da ta gabata, inda bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yerjejeniyar sulhu da fahintar juna.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce ya sami ganin takardun yerjejeniyar wacce ta bukaci bangarorin biyu su dakatar da adawa da juna, sannan kungiyar ONLF zata bi kadin bukatunta ta hanyar siyasa da kuma dokokin kasa. 

Banda haka bangarorin biyu zasu kafa kwamitin hadin gwiwa don gano musabbin sabani tsakanin bangarorin biyu da kuma samar da hanyoyin warwaresu.

Mutanen yankin Ogaden na gabacin kasar Habasha yan kabilar Somali ne. Kuma yankin nasu yana arzikin iskar gas wanda ya kai cubit metre trillion hudu kuma tun shekara 2013 ne wani kamfanin kasar China mai suna POLY-GCL ya tona rijiyoyi biyu a yankin.