Ethiopia Za Ta Dage Visa Ga 'Yan Afirka
Daga ranar 9 ga watan Nuwamba kasar Ethiopia za ta dage Visa ga duk wani dan Afirka dake son shiga cikin kasar
Cikin wata sanarwa da gwamnatin Ethiopia ta fitar a jiya Jama'a, ta ce daga ranar 9 ga watan Nuwamba mai kamawa, duk wani dan kasar Afirka mai son zuwa kasar Ethiopia to baya bukatar Visa, wannan kuma kudiri ne da Piraministan kasar Abiy Ahmad ya dauka domin bunkasa hulda tsakanin kasashen Afirka.
A cewar Piraministan na Habasha, kamaya dukkanin kasashen Afirka suka kusantar junansu su kuma bunkasa tattalin arziki da al'adu na kasashensu.
Abiy Ahmad dai shi ne musulmi na farko da ya riki mikamin Piraminista a kasar ta Ethiopia, bayan darewa kan kujerar Piraministan ya sasanta da makwabciyar kasar Eritrea.
A makon da ya gabata ne Piraministan na Habasha Abiy Ahmad ya yiwa gwamnatinsa garan bawul, inda ya bawa Mata ma'aikatu kimanin guda goma.