An Nada Sabon Fira Minista A Kasar Mauritaniya
Shugaban kasar Mauritaniya ya sanar da sunan sabon fira ministan kasar.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: Shugaban kasar Mauritaniya Muhammad Wuld Abdul-Aziz a jiya Litinin ya sanar da Muhammad Wuld Bashir a matsayin sabon fira ministan kasar domin maye gurbin Yahya Wuld Hademine.
Tun tsawon watanni shida da suka gabata ne aka gudanar da zaben 'yan Majalisun Dokoki a Mauritaniya, kuma gamayyar jam'iyyu masu mulki ta samu nasara a zaben, don haka a jiya Litinin fira ministan kasar Yahya Wuld Hademine ya mika takardar yin murabus dinsa daga kan mukaminsa da nufin ganin an kafa sabuwar gwamnati a kasar.
Sabon fira ministan Mauritaniya Muhammad Wuld Bashir dan shekaru 56 a duniya ya rike ministan man fetur da makamashi a tsohuwar gwamnatin fira minista Yahya Wuld Hadmeen da ta kawo karshe a jiya Litinin.