Shugaban Yan Tawayen Sudan ta Kudu Riek Marcher Zai Dawo Gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33856-shugaban_yan_tawayen_sudan_ta_kudu_riek_marcher_zai_dawo_gida
Kakakin gwamnatin Sudan ta kudu ya bayyana cewa Riek Marcher shugaban kungiyar yan tawayen kasar zai koma gida nan ba da dadewa ba.
(last modified 2018-10-31T02:57:50+00:00 )
Oct 31, 2018 02:57 UTC
  • Shugaban Yan Tawayen Sudan ta Kudu Riek Marcher Zai Dawo Gida

Kakakin gwamnatin Sudan ta kudu ya bayyana cewa Riek Marcher shugaban kungiyar yan tawayen kasar zai koma gida nan ba da dadewa ba.

Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto Lam Paul Gabriel yana fadar haka a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa bisa yerjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin Riek Marcher da  gwamnatin kasar don kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar, ana saran shugaban yan tawayen zai dawo gida a yau Laraba. 

Labarin ya kara da cewa Rieck Marcher zai dawo tare da wata tawagar magoya bayansa kuma zai halarci wani taron sulhi na kasa. 

A bisa yerjejeniyar sulhin da aka cimma da tsohon shugaban yan tawayen dai zai koma kan matsayinsa na mataimakin shugaban kasa na farko.

Wannan shi ne karo na biyu kenan bangarorin biyu suke sulhuntawa amma kuma yaki ya sake barkewa a tsakaninsu tun ba'a aiwatar da sulhunba.

Tun shekara ta 2013 ne kasar Sudan ta Kudu ta fada cikin yakin basasa bayan ballewarta daga Sudan a shekara ta 2011.