Majalisun Dokokin Biyu A Kasar Libya Sun Amince Da Dunkulewa
Majalisun dokoki biyu masu adawa da juna a kasar Libya sun cimma matsaya kan dunkulewa don hada kan kasar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Abdul Salam Nassia daya daga cikin yan majalisar dokokin kasar yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa majalisun biyu sun amince da dunkulewa, da kuma samar da shugaban kasa guda da kuma mataimakan shugaban kasa biyu, wanda da haka suke fatan za'a kawo karshen barakan da ta dade tana addabar kasar.
Labarin ya kara da cewa a rahoton da yan majalisun biyu suka fitar bayan kammala taron nasu a jiya Alhamis, sun amince da zaben firaiminista guda wanda zai kafa gwamnatin hadin kan kasa.
Har'ila yau labarin ya nakalto ofishin majalisar dinkin duniya a kasar ta Libya yana tabbatar da labarin sannan ya kara da cewa ya karbi takardun shaidar an cimma wannan yerjejeniyar daga bangarorin majalisun biyu wato na Tabruq da kuma Tripoli.