'Yan Gudun Hijira 6 Sun Mutu A Kasar Chadi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33893-'yan_gudun_hijira_6_sun_mutu_a_kasar_chadi
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato wata kungiyar farar hula na cewa; "Yan gudun hijirar sun mutu ne a yayin kokawar rabon abinci
(last modified 2018-11-02T15:34:46+00:00 )
Nov 02, 2018 15:34 UTC
  • 'Yan Gudun Hijira 6 Sun Mutu A Kasar Chadi

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ambato wata kungiyar farar hula na cewa; "Yan gudun hijirar sun mutu ne a yayin kokawar rabon abinci

Ofishin hukuma mai kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin sansanin 'yan gudun hijira na Bredjing da ke gabacin kasar Chadi.

Kakakin hukumar 'yan gudun hijirar ta duniya Simplice Kpandji ya ce abin da ya faru yana nuni da yadda 'yan gudun hijirar suke da bukatuwa da taimakon abinci. Kaso 55 % na 'yan gudun hijirar suna fuskantar gagarumar matsala a kasar ta Chadi.

Fada ya barke ne ta hanyar amfani da wukake da adduna a tsakanin wadanda ake suke da tsananin bukatuwa da abincin da kuma wadanda suke cikin kyakkyawan yanayi.

Da akwai 'yan gudun hijira 335,000 'yan kasar Sudan da suke rayuwa a cikin kasar chadi tun daga 2003 daga rikicin Darfur.