Kasar Uganda Na Shirin Gudanar Da Alurar Riga Kafin Cutar Eboda
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33936-kasar_uganda_na_shirin_gudanar_da_alurar_riga_kafin_cutar_eboda
Ma'aikatar kiyon lafiyar Uganda ta sanar da shirinta na gudanar da alurar rika kafin cutar Ebola a yankunan kan iyakar kasar
(last modified 2018-11-04T15:49:55+00:00 )
Nov 04, 2018 15:49 UTC
  • Kasar Uganda Na Shirin Gudanar Da Alurar Riga Kafin Cutar Eboda

Ma'aikatar kiyon lafiyar Uganda ta sanar da shirinta na gudanar da alurar rika kafin cutar Ebola a yankunan kan iyakar kasar

Cikin wata sanarwa da ya fitar Ministan kiyon lafiyar kasar Uganda Jane Ruth Aceng ya ce bisa hadin gwiwar hukumar kiyon lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a gobe Litinin za a fara gudanar da alurar riga kafin cutar ebola a yankunan kan iyakar kasar da jamhoriyar demokaradiyar Congo,don kaucewa barkewar cutar la’akari da yadda ake ci gaba da fuskantar annobarta a makociyar kasar Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

A cewar ma’aikatar lafiyar Uganda yanzu haka za ta fara bayar da rigakafin ne daga kan jami’an lafiyarta musamman wadanda ke aiki gab da kan iyakar jamhuriyyar Demokradiyyar Congo tazarar mil 62 da yankin da ake fuskantar annobar.

Ministan  ya ce yanzu haka sun aike da allurai dubu 2 da dari 1 ga jami’ansu da ke can kan iyakar kasar don bayar da kariya ga lafiyarsu kafin kai tsaye su dawo kan jami’ansu da ke aikin a cikin kasar. 

A ko wata rana dai akwai 'yan kasuwa dake kai kawo wadanda yankuna daga kasar Jamhoriyar Demokaradiyar Congo, lamarin da mahukuntan kasar ke ganinsa a matsayin wani hadari da ka iya yada cutar ebola a kasar ta Uganda.