An kai Harin Kunar Bakin Wake A Kasar Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34007-an_kai_harin_kunar_bakin_wake_a_kasar_somaliya
'Yan sandan kasar ta Somaliya sun sanar da cewa a kalla mutane 17 ne su ka kwanta dama sanadiyyar wani harin kunar bakin wake da aka kai a babban birnin kasar Magadishu
(last modified 2018-11-09T15:33:49+00:00 )
Nov 09, 2018 15:33 UTC
  • An kai Harin Kunar Bakin Wake A Kasar Somaliya

'Yan sandan kasar ta Somaliya sun sanar da cewa a kalla mutane 17 ne su ka kwanta dama sanadiyyar wani harin kunar bakin wake da aka kai a babban birnin kasar Magadishu

Kakakin 'yan sandan kasar ta Somaliya Ali Nur ya ce; An kai harin ne a kusa da ginin hukumar 'yan sanda ta binciken manyan laifuka.

 Bugu da kari kakakin 'yan sandan ya ci gaba da cewa; Dukkanin wadanda harin ya rutsa da su, fararen hula ne.

Kawo ya zuwa yanzu babu wata kungiya wacce ta dauki nauyin kai harin sai dai ana zargin kungiyar al-shabab da hannu wajen kai hare-hare kwantankwacin wannan.

Kungiyar al-shabab dai tana a matsayin barazanar tsaro ga kasar somaliya da kuma kasashen da suke makwabtaka da ita