An Gano Wasu Manyan Kabaruka A Kasar Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34011-an_gano_wasu_manyan_kabaruka_a_kasar_habasha
Mahkuntan kasar ta Habasha ne su ka sanar da gano manyan kabaruka masu dauke da mutane 200 a yankin Aromiya
(last modified 2018-11-09T15:39:13+00:00 )
Nov 09, 2018 15:39 UTC
  • An Gano Wasu Manyan Kabaruka A Kasar Habasha

Mahkuntan kasar ta Habasha ne su ka sanar da gano manyan kabaruka masu dauke da mutane 200 a yankin Aromiya

Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya nakalto 'yan sandan kasar ta Habasha suna sanar da gano makeken kabarin mai duake da mutane 200 wadanda suke da alaka da wadanda aka kashe a yayin fada tsakanin mayakan Liyu da kuma masu kare shugaban kasar Somali Land.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch ta zargi kungiyar ta Liyu mai dauke da makamai da kashe mutane bayan azabtar da su, tare da yi tir da hakan.

"Yan sanda sun fara gudanar da bincike domin gabatar da batun a gaban kotu wacce za ta yi hukunci akan tsohon shugaban yankin da ake kira da Somali Landa Abdi Muhammada.

RIkice-rikicen kabilanci na daga cikin matsalolin da kasar Habasha take fuskanta a halin yanzu wadda kuma Pira Minista Abi Ahmad yake kokarin shawo kanta.