Najeriya: An Saukar Da Kwamandan Rundunar Da Take Fada Da Boko Haram
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34033-najeriya_an_saukar_da_kwamandan_rundunar_da_take_fada_da_boko_haram
Sojojin Najeriya sun sanar da sauya kwamanda mai kula da runduna mai fada da Boko Haram Janar Aba Seiko, da janar Benson Akaneiro.
(last modified 2018-11-11T08:48:57+00:00 )
Nov 11, 2018 08:48 UTC
  • Najeriya: An Saukar Da Kwamandan Rundunar Da Take Fada Da Boko Haram

Sojojin Najeriya sun sanar da sauya kwamanda mai kula da runduna mai fada da Boko Haram Janar Aba Seiko, da janar Benson Akaneiro.

Wannan dai shi ne karo na biyar da rudnunar sojojin Najeriya din ta sauya kwamandojin da suke fada da kungiyar ta boko haram.

A karkashin jagorancin janar Aba Seiko kungiyar ta boko haram ta kashe sojoji masu yawa na kasar kamar kuma yadda ta kai hare-hare a cikin kauyuka da dama.

A cikin watan febrairu na 2019 ne dai za a gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba  Muhammadu Buhari yake bayar da taken samar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabacin kasar.

A zaben da ya gabata ma dai shugaban kasar ta Najeriya ya rika bayar da taken zai samar da zaman lafiya a cikin yankin arewa maso gabacin kasar.