An Sake Samun Yaduwar Cutar Ebola A Kasar Congo
Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Demokradiyyar Congo ta ce a kalla mutane 319 ne su ka kamu da cutar a baya bayan nan
Kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ambato majiyar kasar Demokradiyyar Congo na sanar da yaudwar cutar wacce kawo ya zuwa yanzu ta ci rayukan mutane 198
Majiyar ta kara da cewa wannan shi ne karo na goma da cutar ta bulla a cikin kasar ta Demokradiyyar Congo. A karon farko an sami bullar cutar ne a 1976.
Sai dai mahukuntan sun ce suna fuskantar matsanancin yanayi na isa ga wadanda su ka kamu da cutar saboda yake-yaken da ake yi a yankin a tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai.
A tsakanin shekararun 2013 zuwa 2016 cutar ta Ebola ta ci rayukan mutane 11,000 a cikin kasashe da dama na yammacin Afirka.