Somaliya: An Sami Karuwar Wadanda Su Ka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Harin Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34035-somaliya_an_sami_karuwar_wadanda_su_ka_rasa_rayukansu_sanadiyyar_harin_ta'addanci
Majiyar 'yan sanda a kasar ta Somaliya ta ce ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar harin ta'addancin da aka kai a birnin Magadishu a ranar juma'a, ya karu zuwa 50
(last modified 2018-11-11T08:51:17+00:00 )
Nov 11, 2018 08:51 UTC
  • Somaliya: An Sami Karuwar Wadanda Su Ka Rasa Rayukansu Sanadiyyar Harin Ta'addanci

Majiyar 'yan sanda a kasar ta Somaliya ta ce ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka kwanta dama sanadiyyar harin ta'addancin da aka kai a birnin Magadishu a ranar juma'a, ya karu zuwa 50

Kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin kai wanda baya ga wadanda su ka kwanta dama, ya kuma jikkata wasu mutane 58.

Wasu motoci ne guda biyu da aka makare da bama-bamai su ka tarwatse a kusa da Hotel din sahafi, sai kuma harin kunar bakin wake a gab da kofar shiga Hotel din.

Da akwai manyan jami'an gwmanatin Somaliya wadanda suke rayuwa a cikin wannan Hotel din da aka kai wa harin.

Kungiyar al-Shabab da ta kai harin dai tana a matsayin babbar barazanar tsaro ga kasar Somaliya da kuma sauran kasashen da suke makwabtaka da ita.

Daga 2011 zuwa yanzu hare-haren kungiyar sun ci dubban rayukan mutane a cikin gida da kuma waje.