Wani Harin Ta'addanci Yayi Sanadiyyar Mutuwa Da Raunana Mutane A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34064-wani_harin_ta'addanci_yayi_sanadiyyar_mutuwa_da_raunana_mutane_a_mali
Rahotanni daga kasar Mali sun bayyana cewar alal akalla mutane 3 sun mutu kana wasu 4 kuma na daban sun sami raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai arewacin kasar Mali.
(last modified 2018-11-13T07:51:17+00:00 )
Nov 13, 2018 07:51 UTC
  • Wani Harin Ta'addanci Yayi Sanadiyyar Mutuwa Da Raunana Mutane A Mali

Rahotanni daga kasar Mali sun bayyana cewar alal akalla mutane 3 sun mutu kana wasu 4 kuma na daban sun sami raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai arewacin kasar Mali.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar a wata sanarwa da ma'aikatar tsaro da kula da garuruwa ta kasar Mali din ta fitar ta bayyana cewar a daren jiya Litinin ne wata mota da aka makare ta da bama-bamai ta fashe a kusa da wasu rukunan gidaje a yankin Gao da ke arewacin kasar Mali.

Rahotanni sun ce a yayin harin dai wasu mutane 3 sun mutu kana  wasu 4 kuma da suke aiki da Majalisar Dinkin Duniya sun sami raunuka.

Wata kungiyar ta'addanci da take da alaka da kungiyar Al-Qa'ida ta dauki alhakin kai harin.