Burundi Tana Da Wani Shiri Na Yaki Da Satar Mata Zuwa Saudiya
Mataimakin shugaban kasar Burundi Gaston Sindimwo ya bayyana cewa gwamnatin kasar ta fara shiri na musamman don yaki da satar mata zuwa kasar Saudiyya.
Majiyar radiyo suwahili a nan JMI ta nakalto Sindimwo yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake jawabi a taron yaki da fasakorin mutani a kasar.
Mataimakin shugaban kasar ya bukaci kungiyoyin mata da kuma wadanda suke yaki da wannan annobar a kasar su hada kai da gwamnati don ganin ta sami nasar a wannan shirin.
A nashi bangaren shugaban hukumar yaki da fasakorin mutane a kasar ta Burundi Silvier ya bayyana cewa yawan fasakorin mutane musamman mata zuwa kasashen larabawa musamman kasar Saudiya ya karu a cikin yan shekarun da suka gabata.
Sivier ya kara da cewa da dama daga cikin matan kasar Burundi wadanda suke fama da talauci sun yaudaru da alkawalin da ake masu na rayuwa mai kyau a kasashen na larabawa, wanda daga karshe yake kaisu ga zama bayi a kasashen.