Taron Maulidin Manzon Allah A Kasar Zimbabwe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34092-taron_maulidin_manzon_allah_a_kasar_zimbabwe
An shirya gudanar da zaman taron maulidin manzon Allah (SAW) mai taken musulunci addinin rahma a kasar Zimbabwe.
(last modified 2018-11-14T15:56:54+00:00 )
Nov 14, 2018 15:56 UTC
  • Taron Maulidin Manzon Allah A Kasar Zimbabwe

An shirya gudanar da zaman taron maulidin manzon Allah (SAW) mai taken musulunci addinin rahma a kasar Zimbabwe.

A jiya ne aka gudanar da zaman taro mai taken musulunci addinin rahma a birnin Harare fadar mulkin kasar Zimbabwe.

Ofishin jakadancin kasar Iran a Zimbabwe ne ya dauki nauyin shirya wannan taro da kuma gudanar dashi, a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan shigowar watan Maulidin manzon Allah (SAW).

A wannan taron an gayyaci malaman addinin muslunci na sunna da shi’a da darikoki, kamar yadda kuma an gayyaci malaman addinin kirista, wadanda suke zaune lafiya tare da musulmi a kasar.

An gabatar da jawanai kan tarihin manzon Allah da kuma irin darussan da rayuwarsa take koyar da dan adam, ta fuskar hakuri, tausayi, taimakon marassa galihu, gudun duniya, gaskiya da rikon amana da dai sauransu.