'Yan Bindiga Sun kashe Mutane 7 A Jamhuriyar Afrka Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34125-'yan_bindiga_sun_kashe_mutane_7_a_jamhuriyar_afrka_ta_tsakiya
A ci gaba da kaddamar da hare-haren da 'yan bindiga suke yi a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, akalla mutane 7 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a jiya Juma'a.
(last modified 2018-11-17T02:59:25+00:00 )
Nov 17, 2018 02:59 UTC
  • 'Yan Bindiga Sun kashe Mutane 7 A Jamhuriyar Afrka Ta Tsakiya

A ci gaba da kaddamar da hare-haren da 'yan bindiga suke yi a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, akalla mutane 7 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a jiya Juma'a.

Kamfanin dillancin kasar labaran Faransa ya bayar da rahoton cewa, a jiya majiyoyin tawagar majalisar dinkin duniya a birnin Bangui fadar mulkin jamhuriyar Afrika ta tsakiya sun sanar da cewa, 'yan bindiga sun kashe mutane 7 dukkaninsu fararen hula.

Rahotanni sun yi nuni da cewa 'yan bindigar da suka kai hare-haren suna da alaka ne da kungiyar Anti-Balaka ta mabiya addinin kirista masu tsatsauran ra'ayi.

Bisa rahoton na tawagar majalisar dinkin duniya, hudu daga daga cikin mutanen da aka kashe musulmi ne, yayin da uku kuma mabiya addinin kirista ne, da sua hada har da wani babban malamin addinin kirista na yankin Alindao.