Ana Tsare Da Masu Fafatuka 40 A Masar
Nov 18, 2018 06:39 UTC
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (Human Rights Watch), ta ce kimanin masu fafatukar kare hakkin bil adama 40 ne ake tsare dasu a Kasar Masar.
Rahoton da kungiyar ta (HRW) yau ya ce tun a karshen watan Oktoba ne ake tsare da mutanen a wurare daban daban wadanda ba'a bayyana ba.
Kungiyar ta ce mafi yawan wadanda ake tsare da masu taimakawa ne ko ta fuskan shari'a ko ta tallafi ga iyalen fursunonin siyasa da ake tsare da a kasar.
Kungiyar ta kuma yi kira ga mahukuntan kasra ta Masar dasu gaggauta bayyana inda mutanen suke da kuma sakinsu.