An Kashe Sojojin Afirka Ta Tsakiya Uku
Ricikin gida ya hallaka sojojin Afirka ta tsakiya guda uku.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Bangui ya nakalto majiyar tsaron kasar Afirka ta tsakiya a wannan lahadi na cewa musayar wuta tsakanin sojojin kasar da ya wakana a Bambari dake tsakiyar kasar ya salwanta rayukan sojin kasar guda uku.
Majiyar ta ce rikici ya faru ne a tsakanin kungiyar injiniyoyi na bangaren gine-gine kan yadda za a kashe wasu kudade na ginin wasu gidajen sojojin da kuma yadda za a tabbatar da tsaro har zuwa lokacin kamala wannan gini.
Baya wadanda suka rasa rayukansu, majiyar ta ce akwai wasu sojoji uku na kungiyar Injiniyoyin da suka tura birnin Bambari domin gudanar da bikin ranar Abinci na Duniya da suka jikkata.
A cikin irin wannan yanayi na rashin tabas, an dage gudanar da bikin, da aka kudiri gudanarwa a ranar 16 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki har zuwa wani lokaci na daban.
Tun daga shekarar 2013 ne kasar Afirka ta tsakiya ta fada cikin rikicin kabilanci da na addini bayan juyin milkin da aka yi a kasar, a halin yanzu dai kasar na fuskantar matsalakar tsaro da gudun hijra domin tsira da rayuka.