Najeriya:An Hallaka Manyan Komondojin Boko Haram 2
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34146-najeriya_an_hallaka_manyan_komondojin_boko_haram_2
Dakarun tsaron Najeriya sun sanar da hallaka kakakin kungiyar Boko Haram da shugaban bangaren sadarwa na kungiya ta kungiyar Boko Haram dibangaren Albarnawi a gabashin kasar
(last modified 2018-11-18T15:44:26+00:00 )
Nov 18, 2018 15:44 UTC
  • Najeriya:An Hallaka Manyan Komondojin Boko Haram 2

Dakarun tsaron Najeriya sun sanar da hallaka kakakin kungiyar Boko Haram da shugaban bangaren sadarwa na kungiya ta kungiyar Boko Haram dibangaren Albarnawi a gabashin kasar

Cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan lahadi, Rundunar sojin Najeriya ta ce a wani sumame na hadin gwiwa tsakanin sojojin kasa da na sama suka kai kan mayakan kungiyar Boko haram sun samu nasarar hallaka Saleh Ahmed Saleh mai magana da yawun kungiyar.

Har ila yau a cikin wannan farmaki sojojin sun samu nasarar hallaka Baban Hasan shugaban bangaren sadarwa na kungiyar Boko haram bangaren Al-Barnawi.

Tun a 2009 ne dai kungiyar ta fara kai hare-hare a cikin Najeriya wanda kawo ya zuwa yanzu ta kashe fiye da mutane 20,000 da kuma tilasta wa mutane miliyan 2 da 600,000 yin hijira.

Kungiyar Boko haram din dake samun goyon bayan kungiyar ta'addancin ISIS, a cikin 'watanin baya-bayan nan ta tsawaita kai hare-harenta kan dakarun tsaron Najeriya.